<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ina misalan daraja da ban mamaki da
 Jamalinka ya bayyana, ya Allah, haskena!

[V2]
 2) Ya Allahna Madauwami, kwarjininka ya sa
 In yi maka sujada fa a cikin zuciyata.

[V3]
 3) In ƙaunace ka kullum kuwa, mai iko duka ne,
 Don ka yarda ka zo guna, ka nemi ƙaunata.

[V4]
 4) Ba wani uba na duniya, ba wata uwa kuwa,
 Da za su iya renonmu yadda ka ke mana.

[V5]
 5) Sai abu ɗaya na ke so, in zauna gabanka,
 In ga jamalin haskenka, in dinga sujada.

[V6]
 6) In yi shelar sunanka dai, in riƙa tunani
 Yadda ka ƙaunace ni kuwa, ya Allah mai jinƙai.

[V7]
 7) Ina misalin daraja da ban mamaki kuwa
 Na tsarin dukan hikima wadda ka ayana.</lyrics>
<title>Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki LW9</title>
<hymn_number>9</hymn_number>
</song>